Me Yasa Duk Wannan Akan Yan’uwa Musulmi Yake Faruwa ???
Don Allah Ku Amsa Mun Tambayoyi Na.
A ranar 17/1/2017 jirgin saman sojojin nigeria ya jefa bam a sansanin yan gudun hijira dake kauye a karamar hukumar mulkin (Kala Balge) a jahar Borno. Wanda yayi sanadiyyar mutuwar sama da mutum 200 tare da raunana sama da mutum 90.
A ranar 5/9/2021 sojojin saman nigeria sun jefa bam akan yan uwa musulmi a kauyen (Buhari) a karamar hukumar mulkin yanusari dake jahar yobe. Wannan harin yayi sanadiyyar mutuwar yan uwa musulmi sama da 20 tare da raunana sama da mutum 40.
A watan April na shekarar 2020 jirgin saman sojojin nigeria ya hallaka mutum 17 mata da kananan yara a kauyen Sakotoku a karamar hukumar mulkin (Damboa) dake jahar Borno.
Bayan sati biyu da faruwar wannan, jirgin saman sojojin nigeria ya sake hallaka masu sana’ar kamun kifi mutum 20 a kauyen Kwatar Daban Masara dake tafkin chadi.
Jirgin saman sojoji ya hallaka wata mata da yayan ta 4 a kauyen Sububu dake jahar Zamfara.
Jiya 4/12/2023 jirgin saman sojoji ya jefo bam kan yan uwa masulmai Tijjanawa a jahar kaduna, wanda yayi sanadiyyar hallaka sama da mutum 126
Ni Alhassan Mai Lafia tambayar da nike son nayiwa gwamnatin nigeria da rundunar sojojin saman nigeria shine:
1. Meyasa duk wannan abun yake faruwa a arewa kadai??
2. Meyasa duk wannan akan yan uwa musulmi yake faruwa??
3. Shin rashin kwarewar aiki ne, ko ganganci ne?? Ko ana yakar arewa da musulmi ne a fakaice??
4. Sannan shin wane mataki aka dauka domin magance wannan matsalar tun cen baya?? Wane irin bincike akayi domin sanin gaskiyar me ke jawo faruwar wannan??
5. Shin an biya diyyar rayukan wanda iftila’in ya shafa??
6. Me yasa ba’a hukunta sojojin saman dake wasa da rayuwar al’umma fafaren hula??
7. Sakarkarun shugabannin mu na arewa, kucigaba da kallo ana karkashe mu. Mungode.
Amb. Hussaini Ibrahim Khalil.