Takaitaccen Tarihin Rayuwar Sheikh Ahmadu Tijjani RA Cikamakin Waliyai Kashi Na Tara (9)

CIKAMAKIN WALIYAI (9)

 

TAFIYAR SA ZUWA TILMISAN

 

Hijira tana shekara 1181, a lokacin Shehu Ahmadu Tijjani RTA yana da shekaru talatin da daya a duniya ya tafi “tilmisan”, babban gari a ƙasar Algeria mai ɗauke da al’umma daban-daban saboda tarin albarkar dake cikin sa.

 

A wannan garin ne Shehu Tijjani ya sadaukar da lokacin sa wurin koyar da tafsiri da hadisi da kuma ayyukan sa na Ibada, mutanen garin da malamai suna matuƙar kaunar sa kuma suna girmama shi saboda madarar ilimi da tarin hikimar sa. Jama’a sukan tambaye shi inda ya samo wannan ilimin, sai yace musu “ban samu ilimi na lokaci daya ba kuma ba daga wurin malami daya na samu ba face daga wurin duk wayanda na zauna dasu”.

 

Wannan baiwar na Shehu Tijjani yasa shi samun mabiya daga ciki da wajen tilmisan, wasu suna zuwa ne don neman ilimi, wasu suna zuwa ne don neman albarkar sa saboda sun dauke shi babban Shehi, shi kuwa yana tsawatar musu bisa faɗin haka saboda tawadi’u (ƙas-ƙas da kai) irin nashi.

 

A tilmisan ne Shehu Tijjani yayi mafarki da babban ƙudubin nan kuma gausun zamanin sa mai suna Sidi Abu madyan, ya ganshi a cikin taro yana cewa “wa zai bani kyauta ni kuma in lamunce masa abinda yake so”, Shehu Tijjani yace masa zan baka masaƙil (nau’in lissafin kudi a wancan lokacin) guda hudu kai kuma sai ka lamunce min samun ƙuɗubaniyyatil Uzma, Abu madyan yace na lamunce maka, Shehu Tijjani zai mika masa kudin kenan sai ya farka.

 

Gari yana wayewa ya tafi raudar Abu Madyan yace “ga abinda nayi alkawarin baka amma zan rabawa mabuƙata sai ladan ya iso gareka”, yaje yana raba musu kenan sai wani daga cikin su yace “zan aurar da yarinya bani da kudi sai nayi kamun ƙafa da waliyyin nan Abu Madyan jiya, kaga shine Allah ya bani domin sa”, Shehu Tijjani yayi murmushi kawai ya tafi.

 

✍️ Sidi Sadauki

Share

Back to top button