Takaitaccen Tarihin Sheikh Ahmadu Tijjani RA Cikamakin Waliyai Kashi Na Goma Sha Daya (11)

CIKAMAKIN WALIYAI (11)

 

AIKIN HAJJI DA DAWOWAR SA TILMISAN

 

A Makka ya sadu da babban ƙudubi wato Sidi Ahmad ɗan Abdullahi Al-hindi RTA wanda ya kasance baya fitowa balle a ganshi ko ya ga mutane, sai hadimin sa ɗaya kawai ke iya ganin shi, don haka ya aikowa Shehu Tijjani wasiƙa yana mai sanar dashi cewa “kaine magajin sirrorina da haskena (ma’arifa) da komai nawa”. A lokacin da ya rubuta wannan wasikar, sai ya sanar da hadimin nasa cewa “wannan shine wanda na dade ina jiran tahowar sa, shine magaji na”, hadimin sai ya ce “haba shehi na, ni da na kwashe shekaru sha takwas ina maka hidima baka sanya na zama magajin ka ba sai bako daga magrib”, Sidi Ahmad Al-hindi yace ai zabin Allah kenan, wanda yaso yake ba baiwar sa, inda ace ni ke da ikon zaɓo magaji na, ai ɗa na zan ba tun kafin ka sanni.

 

Sidi Ahmad Al-hindi ya gadar da komai nasa ga Shehu Tijjani sannan ya damƙa amanar karatun ɗan sa a hannun Shehu Tijjani RTA, kana ya sanar da cewa zai bar duniya ranar ashirin ga watan zul hajji, haka kuwa ya faru. Shehu Tijjani yaso ya sadu da shi ido da ido amma yace masa ba zai yiwu ba saboda yanayin muƙamin sa, sai dai yayi mai busharar saduwa da wanda zai hau mukamin sa bayan yayi wafati wato Sidi Muhammad ɗan Abdulkarim Assammani RTA.

 

Bayan Shehu Tijjani ya kammala aikin hajji a makka kuma ya shayar da ɗan Sidi Ahmad Al-hindi ilimomi kamar yadda mahaifin nasa ya bukata, sai ya tafi madina domin ziyartar kakan sa shugaban halitta SAW. A madina ya sadu da Sidi Muhammad Assammani kamar yadda Sidi Ahmad Al-hindi yayi masa bushara.

 

Assammani Ɗarikar sa ta samo asali ne daga Ƙadiriyya, Shazaliyya da khalwatiyya. Ya yiwa Shehu Tijjani iznin ismul A’azam gaba daya da sauran asrarai sannan yace Shehu Tijjani ya tambayi duk abinda yake so, Shehu Tijjani ya tambaya shi kuma ya lamunce mai.

 

Daga Madina sai Shehu Tijjani ya sake dawowa Cairo domin ya ziyarci Sidi Mahamudul Kurdiy, a nan ne ya samu ijazar hadisi da sauran fannonin ilimi daga Sidi Mahamudul Kurdiy saboda ya shirya masa tambayoyi masu wahala a fannonin ilimi kuma Shehu Tijjani ya bada amsoshi gamsassu wayanda suka ƙayatar da malaman misra baki daya.

 

Ya kuma bashi ijazar Ɗarikar Khalwatiyya da ikon shigarwa, koyarwa da tarbiyantar da mutane cikin ta amma Shehu Tijjani bai yarda ba sai Sidi Mahamudul Kurdiy yace masa kar ka damu, kawai ka wadatu da iznin ni kuma zan ji da sauran, daga nan suka yi bankwana, Shehu Tijjani ya koma tilmisan.

 

✍️ Sidi Sadauki

Share

Back to top button