Yau 17 ga watan Safar 1446H, Ɗarikar Tijjaniyya ta cika shekaru 250 da Samuwa. 

SHEKARA 250

 

Yau 17 ga watan Safar 1446H, Ɗarikar Tijjaniyya ta cika shekaru 250 da samuwa.

 

A ranar 17 ga watan Safar 1196H, Manzon Allah SAW ya bayyana ido da ido ba a bacci ba ga Shehu Tijjani, da rana tsaka a garin Abu Samguna na ƙasar Algeria, yace masa “ka ajiye dukkan wuridin darikar sufaye da kake yi, ka yanke alaƙa da kowani waliyyi, daga yau nine shehin ka, nine mai yi maka madadi”.

 

Sannan Annabi ya masa iznin karanta Istigfari 100, Salatil Fatihi 100 kullum, tareda iznin bayar da shi ga duk wanda ya nema, bayan Shekara Huɗu wato 1200H, Annabi SAW ya cika masa sauran ayyukan Ɗarikar Tijjaniyya kamar yadda muka santa a yau.

 

Dan’uwa ga tambaya.

 

1. Yau shekaran ka nawa ka karɓar Ɗarikar Tijjaniyya?

 

2. Wani irin alheri ka samu bayan ka karɓa?

 

3. A yau me zaka yiwa Shehu Tijjani domin godiya bisa kasancewar sa sanadin samun kusancin ka da Allah?

 

Alhamdulillah

Alhamdulillah

Alhamdulillah

 

Duk wanda bai karɓa ba, ina yi masa nasiha ya karɓa, in kusa dashi babu mukaddami, ya kirani a waya in masa izni (08033074901).

 

ALHAMDULILLAHIL LAZI HADANIY

ILA DARIƘI AHMADAT TIJJANIY

 

✍️ Sidi Sadauki

Back to top button