RASUWA

  • Allah Ya Karbi Rayuwar Daya Daga Cikin Manyan Ya’yan Sheikh Modibbo Jailani Yola Sheikh Mustapha

    INNA’LILLAH WA’INNA ILAIHIR RAJI’UN 😭😭

     

    …Duniyar Musulunci Tayi Babban Rashi.

     

    Allah ya yiwa Sheikh Alh, Mustapha Sheikh Modibbo Jailani Rasuwa. Sheikh Sheikh Mustapha shine babban limamin masallacin juma’a na zawiyyan Modibbo Jailani dake Yola.

     

    Shehin malamin ya rasu a daren jiya juma’a a garin Yola dake jihar Adamawa. Za’a gudanar da sallar jana’izan sa yau juma’a 02/09/2022, bayan Sallar juma’a a masallacin Sheikh Modibbo Jailani jihar Adamawa.

     

    Allah ya jikan sa da rahma ya gafarta masa Allah ya karbi shahadar sa albarkacin Manzon Allah SAW. Amiin

     

    Babangida Alhaji Maina

    Founder CEO/MD Tijjaniyya Media News

  • Limamin Masallacin Juma’a Na Tudun Wada Gusau, Sheikh Dalhatu Umar Gatawa Ya Rasu

    INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI’UN

     

    Allah Rayayye Madawwami ya kar6i Rayuwar Limamin Masallacin Juma’a na Tudun Wada, Gusau, Sheikh Dalhatu Umar Gatawa

     

    Ya Rayu Shekaru 115, ya zama Na’ibin Liman Isah Shutaikhu har Shekaru 20, ya cigaba da Ni’ibanci lokacin Liman Muhammad har Shekaru 10,

     

    Daga baya Ya zama Limamin Masallacin Juma’a na Tudun Wada, har Shekaru 16, Wanda shi ne Matsayin da yake rike dashi har zuwa Wafatinsa bayan fama da JINYA Mai tsawo

     

    Babban Abin da Nasani gameda shi cikakken Masoyin Annabi saww Wanda yasa girmansa Kuma Yana baiwa Ilmi Addini Matukar Kula ga Hakuri da Tawadi’u

     

    Allah yasa Aljanna makomarsa, Allah ya kyauta namu Karshe yasa mu cika da Imani, shine Limami Mafi yawan Shekaru a Gusau.

     

    Muna Ta’aziya ga Iyalansa da Almjiransa a madadin kwamitin I’itikafi na Masallacin Tudun Wada Gusau

     

    Abdulhakeem Ahmad Ya’akub Gusau, Sakatare

  • Inna’lillah Wa’inna Ilaihir Raji’un, Sarki Masoyin Manzon Allah SAW Ya Rasu A Jihar Gombe

    Inna’lillah Wa’inna Ilaihir Raji’un 😭😭

     

    Allah ya karbi rayuwar daya daga cikin manyan sarakunan Musulunci kuma dan Tijjaniyya rasuwa a jihar Gombe.

     

    Allah ya yiwa mai martaba sarkin Funakaye Alhaji Ma’azu Muhammad Kwairanga rasuwa.

     

    Mai martaba sarkin Funakaye Alhaji Ma’azu Muhammad Kwairanga mutum ne mai hidimtawa addini Musulunci da tabbatar da gaskiya da adalci a rayuwar sa, matashi wanda ya sadaukar da rayuwar sa wurin taimakon al’ummar sa a koda yaushe.

     

    Za’ayi gudanar da sallar jana’izan sa yau Lahadi 28/08/2022, da misalin karfe 2:00 na yamma a garin Bajuga karamar hukumar Funakaye jihar Gombe.

     

    Allah ya jikan sa da rahma ya gafarta masa Allah ya jaddada masa rahma Amiin.

     

    Babangida A Maina

    National Director Fityanu Media

  • A Rana Irin Ta Yau Ne Aka Gudanar Da Sallar Jana’izan Sheikh Dr, Hadi Sheikh Dahiru Bauchi RA

    TUNA BAYA II A Ranar Jana’izar DR. HADI IBN MAULANA SHEIKH DAHIRU USMAN BAUCHI An ‘Dauko (Gawar Shi) Za’a Sanya Shi a Cikin Kabari,

     

    Sai KHALIPHA (Sheikh) ISMAIL KANO (ALLAH Ya ‘Kara Masa Kusanci Da MA’AIKI (S.A.W) Ya Fashe Da Kuka(Cikin Ban Tausayi) Ya Ce;

     

    “To Jama’ah! Kun Ga Dai Yanda Ake Binne Karatu, Wannan Laburari(Library) Ne Sukutum Ake Shirin Binnewa Anan, Kaico! Da Haka Ake Rasa Ilimi a Duniya”.

     

    Duniya Kenan YAU: Da KHALIPHAN Da DR. HADIN (R.A) Duk Sun Koma Ga Rahamar ALLAH.

     

    ALLAH YA ‘KARA MUSU KUSANCI GA SHUGABA (S.A.W), YA JADDADA MUSU RAHAMA, ALLAH YA MANA IRIN TASU AMEEEN

  • Yana Zargin Wasu Bata-garin Sojojin Najeriya Da Kashe Fitaccen Malami A Gashua.

    Inna’lillah Wa’inna Ilaihir Raji’un 😭😭

     

    …Yana Zargin Wasu Bata-Garin Sojojin Najeriya Da Ka@she Fitaccen Malami A Gashua.

     

    A jiya Asabar ne muka samu labarin rasuwan babban malamin Musulunci a jihar Yobe Sheikh Goni Aisami dake garin Gashua a jihar Yabe rasuwa a hanyar dawowa daga jihar Kano zuwa Gashua.

     

    Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya nuna Damusan sa akan faruwan lamarin tare da nuna baƙin-cikinsa akan ki@san da Akayi wa Sheikh Goni Aisami, a ranar Juma’a.

     

    BBC Hausa sun ruwaito cewa malamin mazaunin garin Gashua da ke karamar hukumar Bade an zargi sojoji da harbe shi a yankin Jaji-Maji da ke karamar hukumar Karasuwa na jihar Yobe.

     

    Kakakin ‘yan sandan jihar, Daungus Abdulkarim, ya ce sojojin biyu da suka yi kokarin sace motar malamin bayan harbe shi an damƙesu.

     

    Gwamna Buni a wata sanarwa da ya fitar a Damaturu, ya ce wannan kisa abin takaici ne da alla-wadai, don haka za a binciki lamarin.

     

    Mai Mala ya ce duk wanda aka samu da laifi za su fuskanci hukunci. Sannan ya miƙa ta’azziyarsa zuwa da iyalan marigayin da al’ummar karamar hukumar Bade da ilahirin jihar kan kisan Aisami.

     

    An gudanar da sallar jana’izan sa kamar yadda addinin Islama ya tanadar a garin Bade dake karamar hukumar Gashua jihar Yobe.

     

    Allah ya jikan sa da rahma ya gafarta masa rahma ya karbi shahadar sa. Amiin Yaa ALLAH

     

    Babangida A Maina

    Tijjaniyya Media News

Back to top button