RASUWA

  • Allah Ya Yiwa Mahaifiyar Sheikh Ibrahim Gajali Dake Jihar Gombe Rasuwa Jiya Juma’a.

    INNA LILLAHI WA’INNA ILAIHI RAJI’UN

     

    Allah yayiwa yadikkon Maulana Shehu Ibrahim Aliyu Gajale rasuwa wacce aka fi sani da Dada Ɗacce a daran yau.

     

    Za’a gudanar da jana’izarta gobe in Allah ya kaimu a ƙofar gidan Maulana Sahibuz Zikiri Wassalati dake pantami layin dogon ƙarfe Gombe, Ƙarfe 03:00pm in Allah ya kaimu.

     

    Allah Ubangiji Ya jiƙanta ya gafarta mata Albarkacin Shugaban Halitta Sallallahu Alaihi Wasallam. Amin

     

    Mustapha Abubakar Kwaro

    Tijjaniyya Media News

  • YANZU-YANZU: Babban Malamin Darikar Tijjaniyya A Najeriya Ya Rasu Sheikh Ibrahim Modibbo Jarkasa Kano.

    Inna’lillah Wa’inna Ilaihir Raji’un 😭😭😭

     

    ….Allah Ya Karbi Rayuwar Sheikh Modibbo Jarkasa Kano Babban Malamin Tijjaniyya.

     

    Allah ya yiwa babban malamin Musulunci kuma shehun Darikar Tijjaniyya a najeriya Sheikh Ibrahim Umar Modibbo Jarkasa Kano rasuwa.

     

    Shehin malamin babban ya bada gagarumar gudumawa a addinin Islama a najeriya dama Africa ya kasance mutun mai tawadi’u, tsaron Allah, tausayin da kuma taimakon Al’umma.

     

    Allah ya jikan sa da rahma ya gafarta masa Allah ya karbi shahadar sa. Amiin Yaa ALLAH

     

    Babangida A Maina

    Tijjaniyya Media News

  • An Gudanar Da Sallar Jana’izan Wasu Bayin ALLAH Da Yan Bindiga Suka Kashe A Taraba.

    Inna’lillah Wa’inna Ilaihir Raji’un 😭😭

     

    Anyi jana’izar wasu daga cikin bayin Allah da iftila’in yan Bindiga ya rutsa dasu a garin Kare kuka dake Gunduma ward a karamar hukumar Gassol A Jihar Taraba.

     

    Anyi Sallar jana’izar kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar a kofar hakimin Gunduma cikin garin Gunduma da fatan Allah ya jikan su ya gafarta musu.

     

    Allah ya karbi shahadarsu ya kawo mana karshen wannan masifar da muke ciki wannan kasa namu Najeriya. Amiin

     

    Daga: Muhammad Abdullahi Tutare.

  • Allah Ya Karbi Rayuwar Daya Daga Cikin Mahajjatan Jihar Kaduna Hajiya Maryam Ahmad.

    INNALILLAHI WA’INNA ILAIHIR RAJI’UNN

     

    Mahajjaciyar Jihar Kaduna Ta Rasu A Kasar Saudiyya

     

    Allah Ya Yi Wa Ɗaya Daga Cikin Mahajjaciyar Jihar Kaduna Wadda Ta Fito Daga Gundumar Igabi Ta Jihar Kaduna, Hajia Maryam Ahmed Rasuwa Ranar Juma’a A Garin Makkah Dake Kasar Saudiya.

     

    Majiyar RARIYA Ta Nakalto Cewa An Yi Jana’izarta A Masallacin Harami Dake Birnin Makkah Na Ƙasar Saudiyya Yau Juma’a.

     

    Allah Ya Jiƙanta Da Rahma Ya Gafarta Mata, Amiin Yaa ALLAH.

     

    Daga Jamilu Dabawa.

  • Inna’lillah Wa’inna Ilaihir Raji’un, Yaya Da Kani Sun Rasu A Hanyar Zuwa Jana’izar Kawunsu.

    INNALILLAHI WA’INNA ILAIHIR RAJI’UN

     

    ….Yaya Da Kani Sun Rasu A Hanyar Zuwa Jana’izar Kawunsu.

     

    Abdul Gajo Shi da dan uwansa Liman Gajo sun rasu ne a hanyar su ta zuwa Jigawa don halarta jana’izar Kawun su Alhaji Habibu Gajo Yalleman da ya rasu a jiya Lahadi, wanda shine tsohon mataimakin dan takarar shugaban kasa a karkashin Jam’iyyar APGA.

     

    Allah Ya Jikansu Da Rahma. Ya Gafarta Masu ALLAH Ya Karbi Bakwancin Su, Amiin

Back to top button