TIJJANIYYA

  • Nasiha Zuwa Ga Daukaci Mutane SHEHU Ahmadu Tijjani RA.

    NASIHA ZUWA GA YAN’UWA TIJJANAWA

     

    Don Allah mu girmama junan mu, Maulana Sheikh Ahmad Tijjani R.T.A. yace alaka mai kyau tsakanin mu.

     

    Yan Tijjaniyya yafi wuridodinta domin su Wuridodinta idan sun wuce zaka iya ramawa Amma idan Alaka ya baci to Fa komai ya lalace

     

    Mu saka Tijjniyyan a gaba fiyeda komai Karka bari wani Abun Duniya yasaka ka barar da Wannan hanya Mai tsadan gaske da Shehu nammu suka dora mu Akai Idan kai.

     

    Dan Tijjaniyya kuka samu sabanin ra’ayi Akan wani Abu na harkar Duniya da wani da’nuwanka karku yarda Wannan Abun ya haifarmuku da gaba a tsakaninku kowa yayi nasa koda a Cikin Tijjniyyan ma dama kowa da

     

    Shehin sa da mashayansa haka itama Sal-salan dariqa kowa da nasa don Allah ya’nuwa mu kiyaye mu girmama Juna karku Raina manya Sirrin a hannun su take muyi biyayya sai mu Samu Albarka Mai yawa Allah shiyi mana Jagora don Alfarmam Ma’aiki S.A.W. Amiin Yaa ALLAH.

     

    Sayyidi Abubakar Ibrahim

    Share
  • ILIMIN TIJJANIYA (Kashi Na Biyu 3) Qa’idodinn Darikar Tijjaniyya

    ILIMIN TIJJANIYA (kashi na biyu)

     

    QA’IDOJIN DARIKAR TIJJANIYA

     

    A’udhu Billahi minash-shaɗanir rajim

    Bismillahir Rahmanir Rahim

    Wa sallallahu alal fatihil khatimil Nasiril Hadiy wa alihi wa sahabihi haqqa qadrihi wa miqadarihil Azim.

     

    7. QA’IDAR SHIGA DARIKA

     

    Wayannan sune qa’idojin da suke wajibi ne mutum ya aminta dasu kafin ayi masa iznin shiga Ɗarikar Tijjaniya.

     

    A. BA A DAINAWA IN AKA KARƁA.

     

    Ma’ana in ka karɓa babu ranar da zakace kai ka gaji ko ka fasa dan haka ba zakayi lazumin da wazifar da zikirin juma’ar ba. Ba a gajiya, ba a fasawa ba a dainawa domin Alqawari ne. Alqawari kuwa abin tambaya ne kuma saɓata suffar munafukai ne.

     

    B. BA A HAƊA TIJJANIYA DA WATA ƊARIKAR.

     

    Wato kamar yadda naga wasu suna yi sai suce su QADIRAWA ne kuma TIJJANAWA ne. A’a sam ba a haɗa ta da wata ɗarikar. Shehu Tijjani a lokacin da Annabi SAW zai bashi wannan darikar, yana riqe da dariku kusan 40 akace amma Annabi SAW yace duk ya ajiye su ya riqi wannan shi kaɗai. Annabi yace masa NINE SHEHINKA NINE MAI YI MAKA MADADI.

     

    C. BA A ZIYARTAR WANI WALIYYI WANDA BA BATIJJANE BANE DAN NEMAN ALBARKA.

     

    Misali kaji ance waliyin Darika kaza yazo gari ko A’a Qabarinsa na wuri kaza bari kuje neman albarkarsa, A’a haka haramun ne. Amma kana iya zumunci da yan’uwanka wayanda suke wata darikar.

     

    HUKUNCI

    Duk wanda ya aikata daya daga cikin sharudda guda uku ɗin nan, ya yanke alaqarsa da tijjaniya sai in har ya sake komawa wurin muqaddami an sake yi masa izni.

     

    8. QA’IDOJIN DAKE INGANTA AIKIN DARIKA.

     

    Bayan ka karbi darika ka kiyaye sharuddan karbarta, toh lazumi da wazifa da zikirin juma’a akwai sharudda guda biyar akan su kamar haka

    A. Niyya: dole kayi niyya yayin da zakayi lazumi ko wazifa ko zikirin juma’a.

     

    B. Tsarkin Jiki: tsarkake jiki daga fitsari da bayan gida da maniyyi da sauransu

     

    C. Tsarkin Tufafi: sanya tufafi masu tsarki ba wayanda shari’a ta haramta ba

     

    D. Suturta Al’aura: Ba a yarda Batijjane ko Batijjaniya suyi lazumi ko wazifa ko zikirin juma’a da tsiraici a waje ba, dole namiji ya rufe cibiyarsa zuwa gwiwar sa, mace ta rufe dukkan jikin ta sai kawai hannayenta da sawayenta da fuska.

     

    E. Rashin magana: yayin da kake lazumi ko wazifa ko zikirin juma’a, ba a son kayi magana da kowa sai dai in da larura waccw shari’a ta yarda da ita.

     

    HUKUNCI

    Duk wanda yayi watsi da ɗaya daga cikin sharuddan nan toh lazumin sa ko wazifarsa ko zikirin juma’ar sa ta lalace. Wajibi ne kuma ya sake yin su cikin kiyaye wayancan sharuddan.

     

    9. QA’IDOJIN DAKE CIKA AIKIN BATIJJANE.

     

    Idan ka kiyaye sharuɗɗa biyar din can na baya da suke iya rusa aikin ka, toh ga wasu masu ɗumbin yawa wayanda zasu sanya aikin naka ya zama karɓaɓɓe har ka samu abubuwan da ake samu na riba. Daga ciki akwai:

     

    A. Fuskantar Alqibla yayin da zakayi lazumi (ko wazifa da zikirin juma’a in kai kaɗai ne ba a jam’i ba).

     

    B. Zama irin na tahiya yayin wuridi. Wato zama da gefen ka na hagu ba zaman harɗe (zaman sarakuna) ba.

     

    C. Da kiyaye salloli biyar cikin jam’i

     

    D. Da biyayya ga iyaye da miji (ga matar aure)

     

    E. Da aikata mai kyau da barin mara kyau

     

    F. Da dawwama cikin son Shehu Tijjani so mai tsanani da son yan’uwanka tijjanawa.

     

    G. Da yawan nasiha ga yan’uwa

     

    H. Da hadarto surar Annabi SAW ko Shehu Tijjani ko shehinka yayin da kake wuridin tijjaniya.

     

    I. Da kakkabe duniya da abinda ke cikinta daga zuciyar ka yayin da kake wuridin tijjaniya.

     

    J. Da fahimtar ma’anar abinda kake fadi yayin wuridi.

     

    Da sauransu…

     

    QARIN BAYANI

    1. Sharuɗɗa uku na farko su kaɗai suke iya fitar da mutum daga tijjaniya ba wani abu ba. Ballantana wani yayi maka barazana yace zai qwace darikar daga gareka in bakayi masa kaza da kaza ba. Saidai akwai manyan waliyai a cikin tijjaniya wayanda in ka taɓa su, tamkar ka taɓa Shehu Tijjani ne, taɓa Shehu Tijjani kuwa, yanke alaqa ne da tijjaniya. Wannan shi ake kira SALBU.

     

    Watarana Shehu Dahiru Bauchi RTA yaje ziyara wurin Shehu Gibrima. Da ya juya zai wuce sai Shehu Gibrima yake cewa mutanen wurin, kunga wannan yaron? Nan gaba za a yiwa manyan shehunnai SALBU in suka taɓa shi.

     

    Haka zalika Shan taba, Zina, ca-ca da sauran laifuka basa fitar da mutum daga tijjaniya amma babu kyau Batijjane ya aikata su.

     

    2. Sharuɗɗa na biyu kuma su lalata aikin Batijjane suke yi.

     

    3. Na uku kuma rashin aikata su baya lalata aikin Batijjane amma yana rage masa tibar aikin.

     

    IN KAGA SUNNA A YAU HASKENTA NA ZAHRA, ZIKIRI SALATI SUNA JERANTUWA KU JIYA

     

    TALLAHI KA GANSU SUNE SUNKA RAYA WAJEN, BAYAN MACEWASSA SHEKARU TILI KU BIYA

     

    Daga: Balarabe Faruk

    (Sadauki Nasidibashir Alfatahiy).

    Share
  • ILIMIN DARIKAR TIJJANIYA (Kashi Na Daya 1)

    ILIMIN DARIKAR TIJJANIYA (Kashi na daya)

     

    A’uzu billahi minash-shaɗanir rajim

    Bismillahir Rahmanir Raheem

     

    Nayi wannan rubutu ne dan yan’uwa su san Darikar Tijjaniya da abinda ta qunsa dan su fahimci abinda suke yi ba abun wasa bane.

     

    1. WAYE SUFI?

     

    Mutum ne musulmi Mumini Wanda Babu Abinda Yake Bukata A Duniya Sai Yardar Allah Da Neman Kusanci Da Manzon Allah SAW. Haka Kuma Baya Kwadayin Aljanna Ko Kuma Tsoron Jahannama, Yana Ibada Ne Dan Godiya Ga Allah Bisa Ni’imominsa Gareshi. Sufi Waliyyi Ne, Amma Ba Dukkan Waliyyi Bane Sufi.

     

    2. MENENE SUFANTAKA?

     

    Shine “Aikata Dukkan Abinda Allah Yakeso A Yadda Yakeso Ba Yadda Kakeso Ba, Da Barin Dukkan Abinda Allah Bayaso Koda Kai Kanaso Tareda Kyautata Zato Ga Allah Da Halittunsa.

     

    3. MENENE DARIQUN SUFAYE?

    Farko ƊARIQA Kalma ce Wacce Take Nufin “HANYA” Ko “TAFARKI” A Harshen larabci.

     

    Darika a musulunci yana nufin tafarkin da za a bi dan Samun Kusanci da Allah da yardarsa cikin sauqi bisa qamun qafa da waliyan Allah.

     

    Allah S.W.T shi yayi umurni garemu akan mubi tafarkin Sufaye inda yake cewa “Wattabi’i Sabila Man Anaba Ilayya” Wato Kubi Tafarkin Wanda Zai Taho Gareni.

     

    Darikun Sufaye guda 313 Yana Da Tushe A Musulunci Kuma Hanyace Ta Samun Shiga Aljanna A Saukake. Annabi SAW Yace “Lallai Shari’ata (musulunci) Tazo Ne Bisa Dariku Guda 313, Duk Wanda Yayi Riko Da Ita (daya daga ciki) Ubangiji Zai Shigar Dashi Aljanna” (Dabarani ya ruwaito hadisin).

     

    4. DARIKAR TIJJANIYA

     

    Tijjaniya itace ɗarika ta qarshe a jerin Ɗariku guda 313 ɗin nan kuma Wanda Allah yaba ragamarta shine Sidi Ahmad bin Muhammad Attijaniy RTA. Cikakken Sharifi, shugaban waliyan Allah baki daya daga farkon duniya zuwa qarshe. Kuma shine cikamakin su baki daya. Annabi SAW ne ya bashi komai na darikar tijjaniya ido da ido ba a bacci ba.

     

    5. ABINDA TA QUNSA DA HUJJOJI

     

    Shehu Ibrahim RTA Yana Cewa: “Darikace Mai Tsantsar Falala Da Samun Yardar Allah Wanda Aka Gina Bisa Sunnar Annabi S.A.W Da Kur’ani”.

     

    Darikar Tijjaniya Babu Komai A Cikinta Sai Abubuwa Guda Uku Kamar Haka:

    A. ISTIGFARI: Allah Yana Cewa “Kayi Tasbihi Ka Godewa Allah Ka Nemi Gafararsa Lallai Shi Allah Mai Karbar Tuba Ne” (Suratun Nasri Aya Na 3). Duk Da Kasancewar Annabi SAW Wanda Baya Laifi Amma A Kullum Shima Yana Istigfari Sau 70 Inji Abu Huraira RA.

     

    B. SALATIN ANNABI: Allah Yana Cewa “Lallai Allah Da Mala’ikunsa Suna Salati Ga Annabi SAW, Ya Ku Wayanda Kukayi Imani Kuyi Salati A Gareshi Da Aminci” (suratul ahzab aya na 56). Annabi SAW Yace “Mutanen Da Suka Fi Kowa A Wurina Sune Mutanen Da Suka Fi Yi Min Salati” tirmizi ya ruwaito shi.

     

    C. LA ILAHA ILLALLAHU: Allah Yana Cewa “Ku Ambace Ni Zan Ambace Ku, Ku Gode Min Kar Ku Kafurce Min” Sannan Annabi SAW Yace “Mafificin Kalma Shine La Ilaha Illallahu”.

     

    6. AYYUKANTA DA HUJJOJI

     

    A. LAZUMIN SAFE DA YAMMA: Allah yana cewa “Kuma Ka Ambaci Ubangijinka Cikin Ranka Kana Mai Kaskantar Da Kai Da Nuna Tsoro Kuma Kana Mai Kas-Kas Da Murya Bada Karfi Ba, Safe Da Yamma Kada Ka Zama Mai Gafala” (Suratul A’araf Aya Na 205)

     

    B. WAZIFA: Itace Hilakuz-Zikiri Wato Da’irar Zikiri. Anas RA Ya Ruwaito Cewa Annabi SAW Yace “Idan Kuka Zo Dausayin Aljanna Ku Tsaya Kuyi Kiwo A Ciki, Aka Tambaye Shi Ina Ne Dausayin Aljanna? Sai Yace Da’irar Zikiri” (tirmizi)

     

    C. ZIKIRIN JUMA’A: Allah yana cewa “Sannan In Kuka Idar Da Sallah Sai Ku Watsu A Kasa Kuna Masu Nema Daga Falalar Allah Sannan Ku Ambaci Allah Ambato Mai Yawa Sai Ku Iya Tsira” (Suratul Juma’ati Aya Na 10.

     

    SADAUKI NASIDI BASHIR ALFATAHIY

    Share
Back to top button