Innalillahi Wa’inna Ilaihir Raji’un; WAYE MUKE BUƘATA A MATSAYIN JAGORA!

WAYE MUKE BUƘATA A MATSAYIN JAGORA!

 

Shehu Ibrahim inyass da Shehu Abul-fathy fa ba rawani suka ɗaura suka nemi waje suka zauna suka ce a zo a girmama su, su ƴaƴan wane kaza bane! aiki sukayi suka hidimtawa wannan Ɗariƙar da rayuwar su da lokacin su da komai nasu😭, Har girman da ganta tazo take girmama su ba tare da sun nema ba🙇

 

Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya shekara sittin da bakwai ( 67 ) wani abu be taɓa faruwa da wani ɗan Tijjaniyya ba a ƙasar nan, ba tare da yaje ya kai musu ɗauki ba. har yau da tsufa ta cimmi shi😭

 

Lokacin faɗa akan wane ne Khalifan Tijjaniyya ko wane ɗan Shehi wane ne! ya ƙare, waye ze tsaya mana idan za a cutar damu ko yayin da aka cutar damu shi ya kamata mu sanya gaba.

 

Waye ze jiɓanci lamarin Tijjaniyya a kasar nan kamar yadda Sheikh Dahiru Bauchi ya jiɓanta tsawon zamani a aikace ba a fade ba

 

Ya ku jagororin mu muna ƙara ga kuyi duk abunda zaku iya a kan wannan lamarin, mu kuma daga nan muna ta yaku da addu’a.

 

Idan akwai abunda kuke so ayi wanda zamu iya a umarce mu, muna shirye.

 

Sheikh Dahiru Usman Bauchi dai tsufa ta cimmasa kuma jikinsa yayi rauni, aikin da yayi a baya ma ya wadatar, lokaci yayi da ya kamata mu fara ganin motsin kowa ta kowanne ɓangare.

 

Wane lefi ƴan’uwan mu su kayi aka kashe su, me yasa jami’an tsaro zasu jefawa ayarin masu Mauludi makami me fashewa ya hallakar da fiye da mutum hamsin..??

 

Gwamnati da jagororin mu ku fito ku bi mana kadun ƴan’uwan mu da aka ka@she a Wajen mauludin Manzon Allah a jihar Kaduna dake kauyen Tudun Biri a karamar hukumar Igabi.

Share

Back to top button