Sayyadi Alhaji Ibrahim Dahiru Bauchi Ya Ziyararci Raudah Sheikh Ibrahim Inyass RTA.

ZIYARA GARIN KHAULAQ

 

Khadimul Faidah Genaral Sheikh Ibrahim Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi RTA ya Ziyararci RAUDAH Maulana Sheikh Ibrahim Niasse RTA da garin Kaulaha dake kasar Senegal.

 

Ziyaran wanda ta kunshi mika ta’aziyyar rashin daya daga cikin ƴaƴan maulana Sheikh Ibrahim Niasse RTA wato Sayyadi Mahmoud wanda Allah ubangiji madaukakin sarki ya karbi rayuwar sa a satin daya gabata. An masa sallah cikin aminci.

 

Allah ya karbi ziyara ya kawo dashi lafiya, Allah ya jikan Sayyadi Mahmoud Sheikh Ibrahim Inyass da rahma. Amiiiin Yaa ALLAH

Share

Back to top button