Yana Daga Cikin Karamar Da Allah Ya Yiwa Maulana Shehu Ahmad Abulfathi RTA

KARAMAR SHEHU ABULFATHI

 

 

Yana daga cikin karamar da Allah ya yiwa Maulana Shehu Ahmad Abulfathi RTA, ya keɓance shi da wasu halaye sannan ya gadar da halayen ga dukkanin Almajiran sa da masoyan sa na gaske, halayen sune:

 

1. RASHIN JAYAYYA: Duk wanda ka gani a halarar Shehu Abulfathi, daga ya’yan sa zuwa almajirai da masoya, ba zaka same su da jayayya ko musu akan abinda bai shafe su ba, shiyasa ake cewa suna da taurin kai, saboda duk abinda shehi ya tarbiyantar dasu a kai, ba zasu saki su kama na wani ba.

 

2. KAWAR DA KAI: Sam ba zaka same su da kula da aibonin jama’a ba ballantana su dinga zurfafa bincike don tono aibobin, in a gaban su zaka yanka ka soya ka cinye, ba zasu kalle ka ba ballantana su kai maganar ka wurin wani.

 

3. WADATAR ZUCI: Yana wahala ka same su da bibiyar mutum don abin hannun sa, hasalima komi talaucin su a zahiri, kallon wadatattu ake musu saboda sirrin wadatuwar halarar Shehu Abulfathi RTA.

 

Wallahi ban dauke maka kowa ba, duk wanda yace maka ya jingina da Shehu Abulfathi kuma ka same shi yana musu da mutane akan sha’anin rayuwa ko addini, ko ka ga yana bibiyar aibobin mutane, ko ka ga yana yawan roƙo da shishigi ga masu kuɗi ko mulki, to ɗayan biyu ne, Imma dai ƙarya yake yi bai da alaƙar ruhi tsakanin sa da shehi, ko kuma halarar shehi bata tare dashi (salbu), Allah ya tsare mu.

 

ALLAH KA ƘARA MANA SOYAYYAR SHEHU ABULFATHI NA HAKIKA, KA GADAR MANA DA SIRRIN SA. Amiiiin Yaa ALLAH

 

✍️ Sidi Sadauki

Share

Back to top button