SAKO ZUWA GA SARKI MUHAMMAD SANUSI DAGA SHEIKH ABDULHAKEEM AHMAD YA’AKUB GUSAU

ZUWA GA SARKI MUHAMMAD SANUSI NA II

 

Assalamu Alaikum,

 

Nata son in Shiru na Kasa, Hasalima sai naji na Kasa Bacci, Kuma Maganar da Zan nada Alaka da Abinda ya faru na carper da Sarki ke takawa har ya Bada Damar Ayi Nazarin Hujjojinsa !!!

 

BAYANIN da Sarki yayi, tun farko da abin Bai faru ba, da ba Bukatarshi da DUK anhuta, Kuma Koda ya faru, ba Mai Zaton Kayi don Wulakanta Sunan Annabi saww. Koda bakay Bayanin ba.

 

Amma dai Ba’a Kiyaye LADABI ba !!! Saboda shi dai DUK Mai SUNA Muhammadu a duniya ya samo NE daga Sunan Annabi saww Wanda ko Kiyaye Alfarmar sa Wajibi ne, KAN Musulmi

 

Da abin ya faru Kuma, Banga Laifin Kayi Bayani ba, don Wayar da Kai, ko Kare Kai, sai dai, Ni

Zatona shi ne, daka gama Bayanin zaka CE: Carpet daga Yanzu an dauketa Kasa, BAZA’A sake takawa ba, bisa dalilai kamar haka:

 

Kafin Nassi zan fara da Hankali:

 

Ni nasani a Fadar Kano Ba’a fadin Sunan Sarki Sanuni 1, sai dai Sarki Khalifa, Ba’a fadin Sunan Sarki Abdullahi sai dai ace: Sarki Alhaji Kuma Kowane Sarki Mahaifiyarsa in za’a ambaceta sai dai a CE Mai Babban Daku don Girmamawa

 

Kuma Ni Inada Yakini idan Akayi Calendar Sarki Khalifa ko Sarki Alhaji ko Shehu Ibrahim Inyass RA, ko Shehu Tijjani RA Sarki sai bazai Taka ba, Yana sane ko da ko badon Wulakantawa ba,

 

Domin da zai faru mu Tijjanawa ba wani Bayani da za’a Muna mu Gamsu ko mugane, to ai DUK Wadannan Sunyi Girma NE da Girman Annabi saww, Kuma yafisu Cancanta da GIRMAMAWA

 

Kuma a Shari’ance:

 

1Qur’ani DUK Inda Allah yace: ولانقربوا yafi kaiwa MATUKA daga cewa: Kar ku aikata laifi KAZA…

 

2 Ya tabbata a Sunnah An Hana Musulmi zuwa Wuraren Tuhuma ko abinda zaka Jawo bayar da Uzuri bayan faruwarsa

 

3. Mu Malikawa NE, Mun San Matsayin Sadduz Zari’ah a Hukunce-Hukunce

 

4. Mai Tsantseni a Addini yakan bar har abinda Babu laifi aikatashi don Gudun fadawa LAIFIN

 

5 Mu MASOYA Annabi saww TARBIYAR da aka Muna akan Ganin Grmansa Zukatan mu da Imanin mu da Ladabinmu Bai Lamuntar haka

 

6. Malamai sun Hana katse kashi da takarda Mai Rubuta Koda Jarida Turanci ce balle Ajami

 

7. Ina son Sarki ya Kara KOMAWA cikin Littafin Asshifa Wajen BAYANIN Wajabbcin Girmama wa da Kiyaye Alfarmar Annabi saww ya Duba

 

8 Imam Shafi’i yace: idan ana Koyi da Mutum idan aikata Makruhi sai yaja an aikata Haram

 

9 MATSAYINKA na Shugaba, Khalifa, Kai yafi Cancanta da Ka Kiyaye LADABI da Annabi saw

 

10. Kuma da ZARAR an dauke Shinfidar an Rataye Maganar ta Kare, Kuma Bai Rageka ba da komi Kuma Ka Karbi Nasiha

 

11 Wadanda suka yada abin ko kan wane Dalili sukayi bashi ne abin KALLO ba, don WANDA YA nisanci SHUBHA Addininsa ya TSIRA

 

12. DUK Wanda Bai FADA Maka haka ba, to ba Masoyika bane, idan Kuma MALAMI NE, a Dora Maka Calender Babansa ko Shekhinsa Ka Rika takawa, kaga ya Zakuyi dashi ?

 

Ina fatar Sarki a Matsayin ka, na Musulmi, Sufi, Batijjane, Khalifa, Masoyi Annabi saww kawai ka Gansu ka dauke CARPET Ka Rataye a Bango yafi Dacewa da LADABI da Soyayyar saww

 

Kuma mu Alhamdulillah Girman kowa Wajen mu ya Ratayane da Girman Annabi saww a Wajensa, SHINE MA’AUNI !!!

 

DUK DAN ADAM, MAI KUSKURE NE, MAFI ALHERIN MASU KUSKURE, MASU TUBA. Hadith

 

ABDULHAKEEM AHMAD YA’AKUB GUSAU

20/RABIUL AWWAL-1446 23/09/2025

Share

Back to top button