WANENE SHEIKH AHMAD TIJJANI ABUL ABBAS RA? TARIHINSA DA RAYUWARSA RTA.
WANENE SHEIKH AHMAD TIJJANI ABUL ABBAS RA? TARIHINSA DA RAYUWARSA RTA
1. NASABARSA RTA
Shine Sheikh Ahmad dan Muhammad dan Mukhtar dan Ahmad dan Muhammad dan Salim dan Abil Idi dan Salim dan Ahmad (Alwaniy) dan Ahmad dan Aliyu dan Abdullah dan Abbas dan AbdulJabbar dan Idris dan Idris dan Is’haq dan Aliyu (Zainul Abidina) dan Ahmad dan Muhammad (Nafsuz Zakiyya) dan Abdullahil Kamil dan Alhasan Musannah dan Alhasan Alhasan Assibdiy dan Sayyidi FADIMA ‘yar Manzon Allah SAWW daga Imam Aliy, RA,
A Wajen Mahaifiya Dan Sayyidi Aisha ne Diyar Abiy Abdullah Muhammad bn Sanusi Attijaniy Almadawiy An haife shi Aini Madiy 13, Safar 1150@H (15, June 1737) yau Shekaru (295)
An Yi masa Aure da Shekaru 15, bayan Shekara daya Mahaifansa biyu sun yi Wafati Rana daya 1166, sai ya Saki Matarsa domin shiga Neman Mazaje Masana Allah don Neman yardarSa
MALAMAN SHEIKH AHMAD TIJJANI RTA
Ya Karanci Qur’ani Wajen Sheikh Abu Abdullah bin Hamwu Attijaniy ya rasu 1162@H ya haddace da Shekaru 7, bayan Kammalawa
Ya cigaba da Neman Ilmoman Shari’a na Tushe da na Rassa har yazama Cikakken Malamin da zai iya koyarwa da yin Fatwa da Shekaru 21
SAURAN SHEIKHANAI DA YA KARBI ILMOMA, ASRARAI, AZKARAI DA AURADAI WAJEN SU DA SHEKARUN WAFATINSU RTA
Sheikh Sayyidi Abu Dayyib bn Muhd 1180
Sheikh Ahmad As Saqaliy Fass 1177
Sheikh Sayyidi Muhd Hasan Alwanjaliy 1185
Sheikh Abdullah bin Sayyidi Arabiy 1188
Sheikh Abul.Abbas Ahmad Dawwash Tazi 1204
Sheikh Sayyidi Abdulkadir bn Muhd
Sheikh Muhd bn Abdullahi Attaziy
Sheikh Mahmudul Alkurdiy Al Iraqiy 1195
Sheikh Ahmad bn Abdullahi Alhindiy 1187
Sheikh Muhd bn Abdulkareem Assammaniy
Sheikh Ahmad Alhabib Algumariy 1166
Sheikh Muhd bn Abdurrahman Al Azhariy 1208
Sheikh Al Arif Muhammad bn Fudail
KADAN DAGA CIKIN DARIQUN DA YA KARBA:
Dayyibiyya Jazuliyya As Shazaliyya
Qadiriyya ya Karba a Fass
Nasiriyya Ashazaliyya
Algumariyya As Siddikiyya
As Sheikhiyya As Shazaliyya
Khalwatiyya
Arrahamaniyya Alkhalwatiyya
Alkhalwatiyya Wajen Sheikh M Alkurdiy RA
KASASHE WASU GARURUWAN DA YA ZAUNA
Kadan daga Kasashen da ya tafi ya ZAUNA don Neman Ilmoma da haduwa da Masana Allah :
Ya fara da Mahifarsa Ainu Madiy, Fass Magrib, Baladul Abyad, Tsakiyar Kusancin Jaza’ir
Tilmisana Zaman Ibada da Karantarwa
Tunis, Masar kan Hanyar zuwansa Hajji
Makkatul Mukarrama da Madinatu Munawwara
Shallah, sai KASRU Abiy Samgoon sai Tuwat
Karshen ya Koma da Fass Nan ya Yi Wafatinsa
KWAREWARSA A FANNOMAN ILMI
Ya Karanci dukkan Fannonan Ilmi na Sharia da Hakika (Sufanci) Kuma ya Kware a dukkansu MusammanTauhidi Tafsiri, Tajweedi, Hadisi da Sufanci Kuma ya karantar dasu sosai da gaske
Sheikhani Zamaninsa sun masa Sheda tare da Sallama mashi
FARA DARIKAR TIJJANIYYA A DUNIYA (249)
Bayan Samun Al Fathul Akbar ya samu tashi Darika Mai Zaman Kanta daga Sayyidil Wujudi 1196 Mai Istigfari 100 da Salati 100 har zuwa 1200 aka cika masa da Haila 100
Ya Hai Mukamin Kudbaniyatul Uzma a farkon Muharram 1214 an Kuma nadashi a Filin Arfa, bayan kwanaki 40, ya Hau Mukamin Khatmiyya da Katmiyya 18 Safar 1214@H
AUREN SHEHU TIJJANI RA A KARO NA BIYU:
Bayan ya cimma Muradinsa na samun yardar Allah ya sakeyin Aure don Koyi da Annabi saw, ya sayi Kuyangi biyu ya ‘yan tasu ya Aure su har sun Haifa masa ‘ya’ya guda biyu
Yayi Wafati a Ranar Alkhamis 17Shawwal 1230
Yanada Shekaru 80, ya bar Mata biyu Sayyida Mabruka da Sayyida Mubaraka da ‘Ya’ya biyu Sayyidi Muhammadul Kabeer da Sayyidi Muhd Alhaeeb an rufe shi a Zawiyyar sa, Fass RTA yau kimanin Shekaru (215)
Sheikh Imam Al Mufty Abu Abdullahi Muhd bn Ibrahim Addakkaliy ya masa Sallah tare dukkan Mutanen Kirki Dake Kasar Algeria.
Ya bar Manyan Waliayai da Manyan Sharifai da Manyan Sheikhunan a Matsayin Khalifofansa. Masha’Allah
Abdulhakeem Ahmad Ya’akub Gusau 30/08/23
13/Safar/1445 @H HAPPY MAULIDIL KHATMI.