Yan bindiga sun kashe Sarkin Gobir Isa Bawa bayan garkuwa da shi

Inna’lillah Wa’inna Ilaihir Raji’un

 

… Allah ya karbi rayuwar sarki Godir Rasuwa a hannun masu garkuwa da mutane.

 

Rahotannin da muke samu daga jihar Sokoto dake arewacin Najeriya ya tabbatar mana da cewa ƴan bindigar da suka yi garkuwa da Sarkin Gobir na garin Gatawa, Alhaji Isa Bawa, sun masa mummanan kisa.

 

A cikin wannan makon ne sarkin ya fito a wani bidiyo yana neman gwamnatin jihar Sokoto ta biya ‘yan bindigar kudin fansa da suka bukata (Kidnapped), inda ya ce idan wa’adi ya cika ba a biya ba za su halaka shi. Subhanallahi.

 

Tsawon sati uku kenan da suka wuce ne ‘yan bin@diga suka yi gar@kuwa da sarkin a yankin kwanar maharba lokacin da yake kan hanya bayan halartar wani taro a cikin garin Sokoto.

 

Gidan rediyon na BBC sunyi hira da, Shuaibu Gwanda Gobir, wanda shi ne magajin garin Gobir, ya ce labari ya ishe su cewa masu garkuwar sun kashe sarkin ne a ranar Talata.

 

Labarin da na samu shi ne ‘yan bindigar sun harbe shi ne tun a jiya [Talata] bayan la’asar, kuma waɗanda suka je tattauna biyan kuɗin fansa ne suka ga gawar sarkin a kwance,” in ji shi.

 

Ya ƙara da cewa zuwa lokacin da aka yi magana da shi ba su samu gawar mai martaban ba tukunna.

 

Allah ya jikan sa ya gafarta masa. Amiiiin Yaa ALLAH

 

Daga: BBC Hausa.

Share

Back to top button