Ƴan bindiga sun ƙi bayar da gawar Sarkin Gobir

Inna’lillah Wa’inna Ilaihir Raji’un.

 

Tun bayan sanar da rasuwan daya daga cikin sarakuna arewacin Najeriya dake kasar Gobir jiya, hankulan mutane da dama a arewacin Najeriya ya tashi kan kisan wulakanci da Yan’ Bindiga suka masa.

 

Masarautar Sabon Birnin Gobir a jihar Sakkwato ta tabbatar sako ɗan marigayi Sarkin Gobir Alhaji Muhammad Bawa Isa da aka sace su tare mai suna Kabiru.

 

Wani mai magana da yawun masarautar Alhaji Shuaibu Gwanda Gobir ya ce an sako shi ne da daren jiya bayan biyan waɗanda suka yi garkuwa da shi da kuma mahaifinsa kuɗin fansar da suka bukata, amma sun ƙi bayar da gawar mahaifinsa inda suka ce sun riga sun binne shi.

 

Yanzu haka dai ɗan nasa na can na karɓar magani a asibiti a garin Sakkwato. Magajin Garin na Sabon Birni ya ce za su yi wa marigayi Sarkin Gobir jana’iza daga nesa wato salatul Ga’ib a yau.

 

Ya buƙaci al’ummar Musulmi a duk duniya da su bi sawunsu wajen yi masa sallar wadda ya ce za su yau.

 

Muna kira da babban murya ga Gwamnati tarayya tare da na jihohin arewacin Najeriya su dauki matakin gaggawa akan yan’ ta’adda dake aikata wanna mummanan aikin a yankin arewacin Najeriya.

 

Allah ya jikan sa da rahma ya gafarta masa albarkan Annabi ﷺ. Amiin

 

Daga: BBC Hausa.

Share

Back to top button