Tarihin Rayuwar Sheikh Ahmadu Tijjani RA (Cikamakin Waliyai) Kashi Na Biyu (2).

CIKAMAKIN WALIYAI (2)

*

NASABAR SA (RTA)

Shehu Ahmadu Tijjani cikakken sharifi ne (Jikan Manzon Allah) wanda nasabar sa take a bayyane saboda kasancewar iyaye da kakannin sa mutane wayanda suka shahara, amma shi kam duk da haka da kuma “salsalar” sa da ya gani a rubuce, bai sakankance ba har sai da ya sadu da Annabi (SAW) Ido da Ido, ya tambaye shi, ya Rasulillahi shin ni jikan kane da gaske? Annabi SAW yace masa kwarai, kai ɗana ne da gaske (har sau uku), yace masa nasabar ka ta wurin Imam Hassan zuwa Imam Aliy da Sayyada Fadima din nan, ingantacciya ce, sannan fa Shehu Tijjani ya samu natsuwa har yake rubutawa da hannun sa mai albarka “Alhassaniy” a gaban sunan sa.

 

Ga Nasabar sa kamar haka:

 

1. TA WURIN MAHAIFIN SA

Shine Sayyadi Ahmadu Tijjani Ɗan Sayyadi Muhammadul Fattah (wanda ake kira Ibn Umar), Ɗan Sayyadi Muhammadul Muktar, Ɗan Sayyadi Ahmad, Ɗan Sayyadi Muhammadu Salim (Na biyu), Ɗan Sayyadi Abil-eed/Abul Ayyad, Ɗan Sayyadi Muhammadu Salim (Na farko), Ɗan Sayyadi Ahmad Alwani, Ɗan Sayyadi Ahmad, Ɗan Sayyadi Ali, Ɗan Sayyadi Abdallah, Ɗan Sayyadi Abbas, Ɗan Sayyadi Abduljabbar, Ɗan Sayyadi Idris (wanda ake kira wusɗa), Ɗan Sayyadi Idris (wanda ake kira Akbar/Dakil), Ɗan Sayyadi Ishaq, Ɗan Sayyadi Aliyu Zainul Abideen, Ɗan Sayyadi Ahmad (wanda ake kira Shabih), Ɗan Sayyadi Muhammad Nafsuz zakiyya, Ɗan Sayyadi Abdallahil kamil, Ɗan Sayyadi Hassanul musanna, Ɗan Sayyadi Hassanus sibɗi, Ɗan Imam Aliy Da Nana Fadima Yar Manzon Allah SAW.

 

2. TA WURIN MAHAIFIYAR SA

Itace Sayyada Nana Aisha ƴar Sayyadi Muhammad Ɗan Sayyadi Muhammadu Sanusi (Allah ya kara musu yarda). Nasabar ta itama yana tukewa ne a gun Sayyadi Idris (Wanda ake kira Akbar, kakan Shehu Tijjani ta wurin uba din nan), a kan shi ne nasabar Shehu Ahmadu Tijjani ta wurin Mahaifiya da Mahaifi ya haɗu, don haka shi jikan Imam Hassan ne ta wurin uwa da uba.

 

ALLAH SABODA TSARKIN WANNAN NASABA, KA TSARKAKE MANA ZUKATAN MU, KA YAYE MANA DUK ABINDA YA DAME MU.

 

✍️ Sidi Sadauki

Share

Back to top button