Annabi Muhammadu SAW Tare Da Dan’uwan Sa Annabi Dawood AS.

ANNABI MUHAMMADU (S.A.W)

 

In Kana Son Ganin Yadda ALLAH(S.W.T) Ya Fifita DARAJAR ANNABI(S.A.W) Fiye Da Ta Kowa, Dubi Yadda Ya Cewa ANNABI DAWOOD (A.S);

 

“فَاحْكُم بَينَ النّاسِ بِالحَق”

 

“Ka Yi Hukunci(Ya Kai Dawood) Tsakanin Mutane Da Gaskiya”,

 

Amma a Haƙƙin ANNABI(S.A.W) Sai Ya Ce Masa:

 

” لِتَحْكُمَ بَينَ النّاسِ بِمَا أَرَاكَ اللَّهُ”

 

“…Don Ka Yi Hukunci(Ya Muhammadu) Da Iyakar Abin Da Ka Fahimta Daga Allah”.

 

Ya Yiwa ANNABI DAWOOD(A.S) Sharaɗi Na Ya Bi Gaskiya,

 

Amma ANNABI MUHAMMADU(S.A.W) Ba Ai Masa Sharadi Ba, Sai Aka Ce Masa Da Iyakar Fahimtarsa Daga ALLAH(S.W.T).

 

Sannan Ya Cewa ANNABI DAWOOD(A.S):

 

وَلاَ تَتَّبِعِ الهَوَى فَيُضِلَّك عَن سَبِيلِ اللَّهِ.

 

Wato: Ya Dawood Kar Ka Bi Son Zuciya; Ya Ɓatar Da Kai Ga Barin Hanyar ALLAH.

 

Shi Kuwa ANNABI(S.A.W) Sai Aka Ce Masa:

 

مَا ضَلَّ صَاحِبُكُم ..

وَمَا يَنطِقُ عَنِ الهَوَى ..

 

“Ai Sam Sam Muhammadu Bai Ta6a Ɓata Ba, Bai San Hanyar Ɓata Ba..

 

…Sa’annan Kwata-Kwata Bai Ta6a Bi Ko Faɗin San Zuciya Ba”,

 

Yayin Da Ake Hana ANNABI DAWOOD (A.S) Ya Kiyayi Bin Son Zuciya, Shi Ko ANNABI MUHAMMADU Tabbatar Wa Ake Yi Bai Ta6a Son Zuciyar Ba.

 

Haka Nan Sanda Ake Ji Ma ANNABI DAWOOD (A.S) Tsoron Kar Ya Ɓata In Ya Bi Son Zuciyar Shi,

 

Shi Kuwa MUHAMMADUR RASULULLAHI, Tabbatar Wa Ake Cewa Bai Ta6a Ɓata Ba, Bai San Hanyar Ɓata Ba, Tun Tale-Tale Har Abadal Abidin.

 

صلوات الله وسلامه عليك يا حبيبي يا رسول الله.

 

(©️Shehi Mai Jamaa✍️)

 

ALLAH Ya ‘Kara Mana ƘAUNAR SAYYIDUL-WUJUDI (S.A.W). Amiiiin

Share

Back to top button