TARIHIN MANZON ALLAH ANNABI MUHAMMADU SAW KASHI NA GOMA SHA TAKWAS (18)

TARIHIN ANNABI MUHAMMAD (SAW) Kashi na 18

 

KAFIREN MAKKA SUNYI NIYYAN KASHE ANNABI (SAW)

 

Daga: Muhammad Yaseen Bin Hussain

 

Bayan ganin yadda Addinin Musulunci yake Kara samun karbuwa da yaduwa a sashin Larabawa, musamman yadda mutanen garin Madina suke Shiga Addinin Musulunci da kuma Alkawarin da Musulman Madina sukayi na cewa zasu kare Annabi Muhammad (SAW) daga duk wata cutarwa, sai Kafiren Garin Makka sukayi ittifaqin Kashe Annabi Muhammad (SAW).

 

Sun zartar da wannan hukunci ne bayan Zama da sukayi da qabilun dake Makka, inda suka yanke hukunci cewa kowace Qabila zata bada Mutum ɗaya sai suyi masa rubdugu gaba dayansu tayadda baza’a gane ɗan wace Qabilace ya kasheshi ba. Idan ba’a gane Wanda ya kasheshi ba kuma, baza’a zargi Qabila daya ba, balle a dauki Mataki a kanta, saidai a zargi dukkan Qabilun ace su biya diyyah.

 

Da Annabi Muhammad (SAW) yasamu labarin wannan Makircin da suka shirya, sai Allah (SWT) yayi masa Umarni yayi hijira cikin wannan daren zuwa garin Madina, nan take Annabi Muhammad (SAW) yayiwa Sayyidina Aliyu bin Abi-Talib (KW/RA) izini daya kwanta a makwancinsa, zuwa washe gari ya wakilceshi kan dukkanin Amanoni da Mutane suka bash,i ya baya kowa ajiyar da ya kawo ajiya gun Annabi Muhammad (SAW). Annabi shikuma ya fita domin Hijira zuwa Madina Kaman yadda Allah (SWT) yayi masa Umarni.

 

Allahu Akbar!, Allah ya Kara mana kaunar Annabi Muhammad (SAW), iyalen gidansa da Sahabbansa, Amin.

 

07032509197

yaseen9253@gmail.com

Share

Back to top button