Ya Kamata Muyi Koyi Da Hakurin ANNABI S.A.W Don Shi Mahakurcine.

Duk masoyin ANNABI S.A.W ya kamata Ya koyi hakuri don ANNABI S.A.W mahakurcine kadan daga hakurici

 

Watarana yana bacci sai wani kafiri yazo ya tada ci yana borin shewa nadade ina nemanka don in kashe ka kuma yau kariyan ka ta kare Ina mai shetanka yau.

 

Wannan Mutumin dai yayi tayin borin sa yagama sai yazaro tokobinsa danufin zai Apkawa ANNABI S.A.W sai nantake wannan tokobin hannun kafirin ya dawo hannun S.A.W

 

Sai yace masa Ni ubangijina yaceceni kaifa waye zai ceceka? Sai makarerren Mutumin yace babu mai cetana

 

YA RASULALLAHI yace mai toh ka karbi musulunci yace baran karbi musulunci ba

 

Sai ANNABI S.A.W yace masa toh me kake so Sai Mutumin yace ka yafeni ka barni in tafi

 

Sai ANNABI S.A.W yace masa na yafeka tashi katafi, Haka ya bashi tokobin sa ya tashi ya tafi kun ga Hakuri irin na ANNABI S.A.W

 

Dan uwana muma muyi Kokari mu Koyi hakuri don musamu yardan ANNABI S.A.W.

 

Allah ka bamu ikon yin Hakuri acikin dukkan Lamuran Mu na yau da Kullum Albarkan ANNABI S.A.W. Amiin Yaa ALLAH.

Share

Back to top button